Zabe bayan kamfe a Yuganda | Siyasa | DW | 17.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zabe bayan kamfe a Yuganda

A ranar Talatan nan ce aka kawo karshen kamfe na 'yan takarar shugaban kasar Yuganda,yayin da jam'iyyu bakwai suka lashi takobin kawo karshen shugabancin shekaru 30 na shugaba Yoweri Museveni.

Yoweri Museveni Präsident Uganda

Shugaba Yoweri Museveni

Shugaban kasar mai ci yanzu Yoweri Museveni da tsohon Firaministana kasar Amama Mbabazi da Kizza Besigye ne dai suka kammala gangamin yakin neman zaben. Hasali ma dai 'yan sanda sun kama dan takarar na adawa Besigye kafin sun sakeshi daga bisani. A kalamansa bayan ya fito da daga ofishin 'yan sanda, Besigye dan takaran babbar jam'iyyar adawa ta FDC na cewa wannan zabe da za'a shiga shi zai kawo karshen mulkin kama karya na shugaba Museveni. Ya kuma lashi takobin daukar matakan a kasa a tsare na kuri'un da ya kira da za su kawo canji.

"Muna da masaniyar cewa akwai yunkurin yin aringizon kuri'u a ranar zabe, to amma ku sani cewa wannan karon da kamar wuya, dan kuwa zamu kasa sanna mu tabbatar mun tsare kuri'un".

Dr. Kizza Besigye Kampala Uganda Proteste

Gangamin kamfe na Kizza Besigye

Wannan dai shine karo na hudu da dan takarar Kizza Besigye ke neman shugabancin kasar Yuganda

To sai dai tuni shugaba Moseveni ya bayyana hangen nasarar lashe zaben karo na biyar, sannan ya gargadi 'yan kasar da suyi hankali da irin kalaman da 'yan adawa ke isarwa a garesu na cewa yana shirin tabka magudi.

"In har ban yi nasaraba zan koma gida in ci gaba da ayyukana, kuma banga dalilin da zai sa inyi magudi a zabe ba, dan kuwa kowa ya sani na lashe zabubbukan da suka gabata a shekarun baya."

Uganda Wahlen Wahlbeobachter der Ostafrikanischen Union Ali Hassan Mwinyi

Ali Hassan Mwinyi me sanya idanu daga kungiyar kasashen Gabashin Afirka

To sai dai tun kan ayi nisa, 'yan kasar suka fara da sa shakku a zukatansu, ga me da irin zafafan kalamai a tsakanin 'yan takarar, don haka ne ma shugabannin addinai a kasar kamar su Sheikh Shabaan Mubajje ke kira ga 'yan kasar da 'yan siyasar da su kaurace wa siyasar zubar da jini dan kawo zaman lafiya da ci gaban kasar Yuganda baki daya.

Shugaba Museveni dai na daga cikin dadaddun shugabannin Afirka da ke kan mulki wanda kuma ya shafe shekaru 30 akan karagar mulkin tun shekara ta 1986. kuma a yanzu yake neman zarcewa.

Sauti da bidiyo akan labarin