Zabe a tsibirin Zanzibar | Labarai | DW | 31.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zabe a tsibirin Zanzibar

Dan sanhin sahiyar yau, jami´an tsaro sun tarwatsa magoya bayan jam´iyar CUF a Zanzibar, dake nuna farin cikin nasara da su ka ce sun samu ,a zaben da a ka gudanar jiya ,a wannan yanki na kasar Tanzania, da ke da dan kwarya-kwarya yanci.

Jami´an tsaro, sunyi anfani da barkonon tsohuwa da kuma ruwan zafi, domin tarwatsa masu zanga-zangar, a birnin Stone Town da ke matsayin baban birnin tsibirin.

Ya zuwa yanzu dai, hukumar zabe ba ta bayyana sakamakon kuri´ar zaben ba, da aka gudanar jiya, inda a kalla mutane rabin million, su ka fito domin zaben shugaban kasa da yan majalisun dokoki.

Mutane 7, su ka samu raunuka a ranar ta jiya, a cikin rigingimun kada kuri´u.

A na sa ran daya daga jam´iyun CCM, mai rike da ragamar mulki, ko kuma CUF mai adawa wata ta lashe zaben.

Jam´iyar CUF a zabbukan 1995, da na 2000 ta yi zargin magudi daga CCM, da ke rike da karagar mulki tun tsawan shekaru 41 da su ka wuce