1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe a kasar Liberia

Hauwa Abubakar AjejeOctober 11, 2005

Daruruwan mutane suka fito jefa kuria a zaben shugaban kasa dana majalisu,karo na farko tun bayan yakin basasa na shekaru 14.

https://p.dw.com/p/BvYw
George Weah
George WeahHoto: dpa - Report

Saoi da dama kafin bude runfunan zabe,daruruwan mutane suka yi jerin gwano tun cikin dare jiya a makarantu,majamiu da wasu cibiyoyin jefa kuria a babban birnin kasar Monrovia da wasu biranen kasar.

Da yawa daga cikinsu,wannan shine karo na farko da zasu fara jefa kuria,kuma sun ganin cewa wata dama ce ta mancewa da yakin basasan shekaru 14 daya lalata kasar tun shekarar 1989.

Wani dalibi da ya jefa kuriarsa karo na farko yace,muna fatar samun shugaba na kwarai wanda zai bamu damar zuwa makakarnta mu kammala karatunmu hakazalika ya samarwa iyayenmu aikin yi.

Cikin yan takara 22 na kujerar shugaban kasa,tsohon dan wasan kwallon kafa na kungiyar AC Milan,George Weah dan shekaru 39,da kuma tsohuwar maaikaciyar bankin duniya Ellen Johnson yar shekaru 66 suke kan gaba a wannan zabe.

George Weah,wanda yake da dinbin magoya baya, ya fito ya jefa kuriarsa a birnin Monrovia,inda ya baiyanawa manema labarai cewa,wannan rana ce mai cike da tarihi a kasar ta Liberia,inda mutane suka fito su nuna yancinsu ba tare da tsoro ba bisa tafarkin demokradiya.

Ellen Johnson da ta fito jefa tata kuria a Tubmanburg,arewacin Monrovia,ta baiyana farin cikinta cewa yan kasar Liberia sun samu yancin zaben shugaba da suke so.

Ellen Johnson idan ta lashe wannan zabe,zata zamo mace ta farko da aka taba zaba a mukamin shugaban kasa a Liberia.

Masu sa ido na kasa da kasa wajen zaben,sun yaba da yadda zaben yake gudana ba tare da wata tangarda ba.

Mai sa ido na Kungiyar taraiyar Turai,Max Van Den Berg,yace,masu jefa kuria a Liberia sun nuna darasi ga shugabanninsu,yadda suka jefa kuriar tasu cikin lumana ba tare da hayaniya ba,ya kuma yaba da yawan mutane da suka fito jefa kuriar.

Cikin yan takarar kujerar shugaban kasar kuwa har da wakilin tsohon shugaban kasar Charles Taylor,wadda ake nema da laifin aikata laifukan yaki akan makwabciya Saliyo.

Tsohon shugaban yan tawaye Sekou Conneh,wanda dakarunsa suka fafata dana Charles Taylor,shima yana daya daga cikin wadanda suka tsaya takarar kujerar shugaban kasar.

Samun nasara wannan zabe dai ya dogara ne akan samun lashe mafi yawa na kujeru 36 na majalisar dattijai da kuma kujeru 64 na majalisar wakilai,wadanda suma a yau ake zabensu.

Kasar ta Liberia mafi dadewa da yancin kanta a nahiyar Afrika,wadda kuma tsoffin bayi bakar fata na Amurka suka kafa ta,ta samu kanta cikin yakin basasa na tsawon shekaru 14, inda aka yi anfani da yara kanana dauke da makamai suna shan miyagun kwayoyi suna masu aikata taasa iri dabam dabam.

Akalla mutane dubu 250 suka rasa rayukansu kuma akalla kashi daya bisa uku na jamaar kasar suka tsere daga gidajensu cikin wannan yaki,hakazalika anyi hasarar dukiyoyi da dama tare da tada hankulan kasashe makwabta.

Har ya zuwa yanzu,babu hasken wutar lantarki ko tsabtaccen ruwan sha a babban birnin kasar,Monrovia.

Daga birnin Newyork Kofi Annan babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya,yayi kira ga yan Liberia da su fito kwansu da kwarkwatarsu su jefa kuriarsu cikin wannan zabe.

Jamian diplomasiya na Afrika sunce, gudanar da wannan zabe cikin lumana, yana da muhimmanci ga kare martabar Afrika.

Irfan Rahman shugaban tawagar sa ido ta AU,yace wannan zabe zai tabbatarwa da sauran yan Afrika cewa,Afrika zata iya gudanar da harkokinta bisa tafarkin demokradiya ba tare da tashin hankali ba.

Masu sa ido na kasa da kasa fiye da 400 suke sa ido a wannan zabe,ciki har da tsohon shugaban kasar Amurka Jimmy Carter.