Zabe a hadaddiyar daular larabawa | Labarai | DW | 16.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zabe a hadaddiyar daular larabawa

A yau ne wasu zababbun masu kada kuriu suke gudanar da zabe ,domin zaban majalisar mashawartar hadaddiyar daular larabawa,wanda ke zama irinsa na farko ,da kirkiro wannan kasa dake yankin Gulf a shekasrata 1971.Sarakun masarautu guda 7 na kasar ne suka zabi mutane 6,500,wanda ke wakiltan kasa da kashi daya daga cikin dari na yawan alummomin kasar,domin zaban rabin wakilan majalisar kasar guda 40.An fara rukunin farko na wannan zabe ne a yau fadar masarautar kasar dake Abu Dhabi kana da masarautar Fujairah.Anasaran gudanar da zabubbukan sauran masarautu biyar,da suka hadar dana cibiyar cinikin kasar,watau Dubai, a ranakkun litinin da laraba.