Za a yi zama na musamman kan Siriya | Labarai | DW | 08.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a yi zama na musamman kan Siriya

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani zama na musamman a ranar Juma'ar da ke tafe domin tattaunawa kan karuwa fadan da ake cigaba da samu a yankin Idlib da ke arewa maso yammacin kasar Siriya.

Kasashen Beljiyam da Jamus da kuma Kuwait ne suka bukaci da a yi wannan zama bayan da Rasha da kuma gwamnatin Siriya din suka matsa kaimi wajen yin luguden wuta a wuraren da masu da'awar jihadi ke rike da su, batun da ya janyo lalacewar asibitoci da makarantu a yankin.

Kimanin mutane miliyan 3 ne ke zaune a birnin na Idlib wanda shi ne birni na karshe da a halin yanzu ba ya karkashin ikon gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.