1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shirya zama don kaucewa afkuwar bala'i a Idlib

Ramatu Garba Baba
September 5, 2018

A yayin da rundunar sojin Siriya ke cikin shiri don kai farmaki kan tungar 'yan tawaye da ke rike da yankin Idlib, shugabanin Rasha da Iran da kuma Turkiya sun shirya wani taro don shawo kan matsalar.

https://p.dw.com/p/34JRF
Bildergalerie Straßenverkehr
Hoto: picture-alliance/AA/H. Muhtar

Taron zai gudana ne a ranar Juma'a mai zuwa don samar da shawarwari na magance matsalar da ta kunno kai na son karbe ikon yankin na Idlib daga hannun 'yan tawayen ta hanyar amfani da karfi. Zaman da ake shirin yi a birnin Tehran na kasar Iran na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suka yi gargadi kan daukar matakin da suka ce ka iya haifar da asarar rayuka na dubban fararen hula da ke rayuwa a wannan yankin. An dai kiyasta cewa dubban 'yan tawaye da suka tsere daga wasu sassan kasar mai fama da rikici ne ke samun mafaka a yankin.