Za a yi jana′izar Akbar Hachemi Rafsandjani | Labarai | DW | 10.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a yi jana'izar Akbar Hachemi Rafsandjani

Gomai na dubban jama'a ne a Iran aka shirya nan gaba a yau za su halarci jana'izar tsohon shugaban kasar Iran Akbar Hachemi Rafsandjani a birnin Téhéran.

Jagoran addinin Ayotollah Al Khamenei shi ne zai jagoranci jana'izar ta daya daga cikin tsofin shugabannin na Iran wanda ake yi wa kalon mai sassucin ra'ayi, wanda 'yan kasar ta Iran da dama ke cewar an yi rashi.Rafsandjani ya rasu yana da shekaru 82 a duniya a ranar Lahadin da ta gabata.