1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A nemi a hukunta masu laifin kisan 'yan Rohingya

Ramatu Garba Baba
November 11, 2019

Kungiyar gamayyar kasashen musulmi ce ta maka gwamnatin kasar Myanmar a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta ICC bisa zargin aikata kisan kiyashi a kan al'ummar musulmin Rohingya.

https://p.dw.com/p/3Sqzl
Bangladesch Rohingya Flüchtlinge Cox’s Bazar | Protest gegen Rückführung
Hoto: picture-alliance/AP Photo/D. Yasin

Kungiyar da kasar Gambiya ta wakilta a shigar da karar, ta zargi mabiya addinin Buddha da laifin karya dokar kasar, ganin yadda ta farma 'yan kabilar da ke zaune a jihar Rakhine, inda aka tafka asarar rayuka. Kungiyar na son ganin an gudanar da bincike don daukar matakin shari'a kan wadanda keda hannu a kisan.

 

Ana sa ran soma shari'a a watan Disamba mai zuwa. Kungiyar na son ganin an kawo karshen musgunawar da ake yi wa 'yan tsirarrun a Myanmar. Rikicin na shekarar 2017, ya tilasta wa 'yan Rohingya kusan miliyan daya zama 'yan gudun hijira, inda suka nemi mafaka a Bangladesh da ke makwabtaka da kasar.