1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: Za gurfanar da masu bore a gaba kotu

Abdourahamane Hassane
November 25, 2022

A kasar Chadi a ranar Talata mai zuwa za a gurfanar da wasu mutane 400 a gaban kotu.

https://p.dw.com/p/4K5vK
Tschad N'Djamena | Demonstration von Anhängern der NGO Wakit-Tama
Hoto: Blaise Daruistone/DW

Mutanen wadanda ake tsare da su tun a lokacin zanga-zangar nuna kyama ga gwamnatin Mahamat Idriss da 'yan adawar suka yi wacce a ciki fiye da mutane 50 suka mutu ana zarginsu da tayar da fitina. Za a gudanar da shari'ar ne kamar yadda ofishin mai shigar da kara na N'Djamena ya sanar a cikin gidan kurkukun da ake tsare da mutanen a Koro Toro, a tsakiyar hamada mai nisan sama da kilomita 600 a arewa maso gabashin babban birnin kasar.