1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a yi wa sojoji shari'a kan kisan gilla

Ramatu Garba Baba
June 24, 2019

Ma'aikatar tsaron kasar Kamaru, ta ce za ta soma gudanar da shari'a kan sojojin kasar 7 da aka zarga da laifin kisan wasu mata biyu da 'ya'yansu a watan Yulin shekarar 2018.

https://p.dw.com/p/3L0tC
Kamerun Amchide Armee Soldaten Anti Boko Haram 11/2014
Hoto: Reinnier Kaze/AFP/Getty Images

Mai magana da yawun ma'aikatar Cyrille Serge, ya ce za a gurfanar dasu don amsa tambayoyi kan zargin hada baki wajen aikata kisan gilla tare da cin amanar kasa. A bara ne aka yi ta watsa hoton bidiyo a kafofin sada zumunta na zamani, da ya nuna wasu da kayan sojoji suna harbe mata da yara. Lamarin da ya sa gwamnatin Kamaru kaddamar da bincike kan sahihancin bidiyon.