Za a shirya zaben gaba da wa′adi a Aljeriya | Labarai | DW | 19.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a shirya zaben gaba da wa'adi a Aljeriya

Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya sanar da rusa majalisar dokokin kasar, hakan dai zuwa ne a matsayin sharar fage a gudanar da zabukan gaba da wa'adi a kasar.

Shugaba Abdelmadjid Tebboune ya kuma ba da umurnin yin afuwa ga masu fafutukar nuna adawa da ke tsare bayan da ya rusa majalisar dokokin kasar. An dai kafa majalisar dokokin mai ci a yanzu ne tun a shekarar 2017 bisa wa'adi na shekaru 5 tare da shirya zabukan na 'yan majalisa a shekarar 2022.

Ko da yake shugaba Tebboune bai sanar da lokacin da za a gudanar da zaben ba , amma dai ana hasashen cewa wala'allah ya gudana tsakanin watan Juli da Satumbar wannan shekarar.

Shugaban na Aljeriya ya karfafa gwiwar matasan kasar kan su fito a dama da su wajen tsayawa takara tare da yin alkawarin biyan kudaden yakin neman zabensu.