Za a sake zama kan shirin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 07.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a sake zama kan shirin nukiliyar Iran

Shirin nukiliyar ta Iran mai cike da cece ku ce, ana son tsaida shi aƙalla tsawon shekaru goma kafin sassauta takunkumin tattalin arziki da aka sanya wa Iran.

Wien - Atomgespräche mit dem Iran

Mahalarta taron nukiliyar Iran

Sakataren harkokin wajen Birtaniya Philiph Hammond ya bayyana cewar zai sake komawa kan tattaunawar da ake yi kan shirin nukiliyar Iran a Vienna a daren gobe Laraba, sannan manyan ƙasashen da ke cikin wannan tattaunawa ana sa ran su sake zama a ranar Alhamis. Mista Hammond ya fada wa manema labarai cewar a daren gobe Laraba za su tabbatar da tattauna abubuwa da dama kafin ranar Alhamis su cimma matsaya

Ƙasar ta Iran da manyan ƙasashen duniya shida masu karfin fada aji Birtaniya da China da Faransa da Jamus da Rasha da Amirka na duba matsaya da za su cimma kan shirin nukiliyar ta Iran mai cike da cece ku ce, da ake son tsaidawa aƙalla tsawon shekaru goma kafin sassauta takunkumin tattalin arziki da aka ƙaƙabawa ƙasar ta Iran.