Za a rantsad da shugaban kasar Zanzibar. | Labarai | DW | 02.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a rantsad da shugaban kasar Zanzibar.

An fara shirye-shiryen rantsad da shugaban tsibirin Zanzibar, Amani Abeid Karume, wanda ya sake cin nasara a zaßen da aka gudanar a karshen makon da ya gabata. Amma `yan jam’iyyun adawan tsibirin sun ce za asu ci gaba da zanga-zangarsu ta nuna adawa da sakamaokon wannan zabe, wanda suka ce an tabka magudi a lokacin ka da kuri’un.