Za a kammala taron sulhunta rikicin Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 02.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a kammala taron sulhunta rikicin Sudan ta Kudu

Bangarorin da ke rikici da juna a kasar zasu tattauna tsakaninsu don kammala yarjejeniyar sulhun da ya samu tsaiko kwanaki kalilan kafin kaddamar da gwamnatin hadaka.

Shugaba Salva Kiir na kasar tare da jagoran 'yan tawaye Riek Machar da kuma wasu kungiyoyi ne suka haifar da jinkirta kammaluwar sulhun tun a watan Satumbar bara, duk kuwa da cewar sun gaza warware matsalolin da ke tsakanin bangarorin biyu da suka jefa kasar a tsaka maiwuya. Bangaren gwamnati dai ya jaddada bukatar taron ya mayar da hankali kan kafa gwamnatin hadaka, yayinda bangaren 'yan tawaye ya bukaci karin watanni shidda kafin hadakar domin samun sukunin kammala warware al'amuran tsaron da suka shafi dawowar Riek Machar kasar. Taron kammala yarjejeniyar sulhun dai zai gudana ne a birnin Addis Ababa na kasar Habasha a wannan rana ta Alhamis.