Za a kai agaji ga mabukatan Siriya | Labarai | DW | 09.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a kai agaji ga mabukatan Siriya

Gwamnatin kasar Siriya ta bada izini ga kungiyoyin da ke aikin agaji da su kai kayan abinci a wurare 19 da aka killace a cikin wannan watan da muke ciki.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Syrian Staffan De Mistura, ya nuna da cewa yana kyautata zaton motocin kai kayan za su isa wuraren da ake tsammani a cikin lokaci. Dubban 'yan kasar Siriya ne dai ke fama da tsananin yunwa, kuma basa samun agaji daga kungiyoyin bada tallafi, sakamkon yadda gwamnati da 'yan tawaye suka killace yankunan da suke iko da su, a matsayin neman mika wuya ga abon kan gaba.