Za a kaddamar da asibitocin gwajin jinyar Ebola | Labarai | DW | 13.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a kaddamar da asibitocin gwajin jinyar Ebola

Kungiyar Likitoci masu ba da agaji ta Medicins Sans Frontieres za ta fara gwajin magungunan Ebola a yammacin Afirka

Kungiyar Likitoci masu ba da agaji ta kasa da kasa wato Medicins Sans Frontieres ta ce za ta kaddamar da asibitoci na gwajin jinya cutar Ebola a yankin yammacin Afirka. Gwaje-gwajen da za a yi kan marasa lafiya don radin kai, za a fara ne a cikin watan Disamba a wasu wurare biyu cikin kasar Guinea sai kuma wani wurin na uku da ba a zayana ba tukuna. Ana sa ran samun sakamakon gwaje-gwajen a cikin watan Maris na shekara mai zuwa. Kungiyar ta Medicins Sans Frontieres ta ce za ta yi gwaje-gwajen da magungunan Favipiravir da Brincidofovir sai kuma wanda za a yi amfani da jinin wadanda suka warke daga cutar Ebola saboda garkuwar da suke da ita. Alkalumman Hukumar Lafiya ta Duniya WHO sun nuna cewa Ebola ta yi sanadin mutuwar mutane 5160 sannan fiye da dubu 14 sun kamu da kwayoyinta a cikin kasashe takwas.