Za a je zagaye na biyu a zaben Laberiya | Labarai | DW | 07.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a je zagaye na biyu a zaben Laberiya

Babbar kotu dai a kasar Laberiya ta ce babu gamsassun bayanai da za su sa a sake zaben baki daya kamar yadda aka shigar mata da korafi.

George Weah (Chris Hondros/Getty Images)

George Weah dan takarar shugabancin Laberiya

Babbar kotun koli a kasar Laberiya ta bayyana a wannan rana ta Alhamis cewa shedu da ta tattara game da zargin magudin zabe a zaben kasar da aka yi a watan Oktoba, ba su gamsar da kotu ba ta bada umarni a sake zaben kasar, abin da zai bude kofa a tafi zagaye na biyu tsakanin 'yan takara tsohon tauraroron wasan kwallon kafa George Weah da mataimakin shugabar kasa Joseph Boakai.

Mai shari'a Philip Banks da yake bayyana hukuncin kotun ya ce shedu da kotu ta tattara ba za su sanya a ce za a sake zaben bakin dayansa ba.