Za a je zagaye na biyu a zaben Laberiya | Labarai | DW | 16.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a je zagaye na biyu a zaben Laberiya

A ranar 7 ga watan Nuwamba mai zuwa ne za a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Laberiya kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.

Bukatar zuwa zagaye na biyu na zaben shugaban kasar ya taso ne bayan da aka gagara samun dan takara da ya iya lashe fiye da kashi 50 cikin 100 na kuri'un da ake bukata. Za a kara ne a wannan zagayen a tsakanin tsohon gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya George Weah da mataimakin shugaban kasa na yanzu Joseph Boakai da suke kan gaba a zagayen farko na zaben da aka fafata a tsakanin 'yan takara 20.

Weah ya samu kashi 39 cikin 100 na kuri'un da aka kada yayin da Boakai ya samu kashi 29 cikin 100, duk wanda ya lashe zaben a zagaye na biyu a tsakanin 'yan takarar biyu, shi zai maye gurbin Shugaba Ellen Sirleaf Johnson mace ta farko da ta taba zama shugaba a Afirka.