Za a gudanar da bincike kan rikicin Gaza | Labarai | DW | 23.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a gudanar da bincike kan rikicin Gaza

Hukumar kare hakkin bani adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da fara gudanar da bincike kan irin luguden wutar da Izra'ila ke yi a Gaza sakamakon rikicinta da Hamas.

Wannan dai ya biyo bayan korafin da Falasdinu ta gabatar gaban hukumar mai mambobi 46, inda 29 daga cikin mambobin da suka hada da kasashen Larabawa da Rasha da China da kasashen Latin Amirka da na nahiyar Afirka sun amince da gudanar da binciken.

To sai dai Amirka ta kada kuri'ar kin amince da kudurin yayin da kasahen Turai galibinsu na kungiyar EU suka yi rowar kuri'unsu. Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da kasashen duniya ke cigaba da neman ganin an kawo karshen zub da jinin da ake yi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar