Kotun ICC za ta fara shari'ar tsohon shugaban Philippines
January 26, 2026
Talla
Alkalan kotun hukunta manyan laifuka na ICC da ke birnin Hague, sun yanke hukuncin cewar, watan Febrairu ne tsohon shugaban Philippines Rodrigo Duterte zai gurfana agaban a kotun, tare da watsi da hujjojin cewa mai shekaru 80 din ba shi karfin fuskantar shari'a.
A ranar 23 ga Fabrairu ne dai Duterte zai fuskanci shari'ar tabbatar da tuhume-tuhumen da ke kan shi, inda alkalai za su yanke hukunci ko zarge-zargen masu gabatar da kara sun isa hujjar ci gaba da shari'a a kansa.
Masu gabatar da kara na ICC sun tuhumi Duterte da laifuka uku na cin zarafin bil'adama, suna zarginsa da hannu a kisan kai 76 a matsayin wani bangare na yakinsa da miyagun kwayoyi.