1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

ICC ta samu Ali Kosheib da laifukan yaki

Abdourahamane Hassane
October 6, 2025

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta samu wani jagoran mayakan sa kai na kasar Sudan da laifukan cin zarafin bil adama a yakin basasar da ya gudana shekaru 20 da suka gabata a yankin Darfur.

https://p.dw.com/p/51ZMN
Ali Kosheib
Ali KosheibHoto: International Criminal Court/Handout/AA/picture alliance

Ali Mohamed  Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kosheib, an same shi da laifuka da dama, da suka hada da fyade, da kisa da azabtarwa, a  yakin Darfur da aka yi  tsakanin shekara ta  2003 zuwa 2004.

Alkali mai gabatar da kara na kotun ya zargi Kosheib,  da kasancewa babban jigo a kungiyar  Larabawa, ta Janjaweed, da kuma taka rawar gani wajen aikata laifuka cin zarafin bil Adama.

Ali Mohammed Kosheib,   wanda ya kai kansa a kotun a shekara ta 2020 domin ta wankeshi daga zargin da ake yi masa

Nan gaba ne, kotun taICC za ta bayyana hukuncin da ta yanke masa.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, rikicin na Darfur da ya kawo karshe a shekarar  ta 2020. ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 300,000 tare da raba miliyan 2.5 da muhallansu.