Za a fara binciken Ebola a kan matafiya | Labarai | DW | 18.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a fara binciken Ebola a kan matafiya

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi kira ga hukumomin kasashen dake fama da cutar Ebola da su shirya gwaji ga masu bulaguru kafin su hau jirgi.

Hukumar lafiya ta duniya WHO mai cibiya a birnin Geneva, ta yi wannan kira ne a yau din nan Litinin (18.08.2014) ga hukumomin dukkanin kasashen dake fama da cutar Ebola, ta yadda za'a tantance lafiyar matafiya dangane da wannan cuta mai saurin yaduwa ta Ebola, a wani mataki na neman takaita yaduwarta ya zuwa wasu sassan da bata fara bulla ba.

Hukumar ta WHO ko OMS ta kara da cewa, duk wanda ke dauke da cutar ta Ebola baza'a bari ya yi bulaguro ba. Sai dai kuma idan bulaguron nasa na da nasaba ne da batun neman lafiyar wanda shima kuma sai likitoci sun tsarashi cikin ka'ida. Ta kara da cewa ko ma da yake hadarin kamuwa da cutar yayin bulaguro bashi da yawa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe