Za a cigaba da maida Qatar saniyar ware | Labarai | DW | 05.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a cigaba da maida Qatar saniyar ware

Ministocin harkokin waje na Saudiyya da Masar da Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa sun nuna rashin jin dadinsu bayan da Qatar ta yi fatali da bukatun nan da suka gabatar mata wanda suke so ta cika kafin su daidaita.

A wani sako da ya gabatar a madadin kasashen hudu, ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukri ya ce ko kusa Qatar ba ta nuna alama ta sauya matsayin da ta dauka ba tun bayan da aka mika mata wadannan bukatu da suka hada da yanke hulda da Iran da kuma rufe gidan talabijin na Al-Jazeera.

Da ya ke nasa jawabin ministan harkokin wajen Saudiyya ye ce tunda ba wani abu sabo da suka gani, kasashen sun yanke shawarar cigaba da maida Qatar din saniyar ware ta fuskar diflomasiyya sannan kuma ba za su cigaba da damawa da ita ta fuskar tattalin arziki ba sai dai ya ce ba za su kara daukar wasu karin matakai kan kasar ba. Ya zuwa yanzu dai hukumomi a Doha ba su kai ga maida martani ba kan wannan matsaya da wadannan kasashe da ke zaman doya da manja da kasarsu suka dauka ba.