1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a binciki harin Guba a Siriya

Abdul-raheem HassanSeptember 8, 2016

Majalisar Dinkin Duniya za ta binciki sahihancin rahotannin hukumar kiyaye amfani da makaman guba, da ke zargin dakarun gwamnatin Siriya da kai harin guba a garin Sukuri.

https://p.dw.com/p/1JxV4
Syrien Truppen der Opposition greifen Stellungen des IS nahe Aleppo an
Hoto: picture-alliance/dpa/Anadolu/H. Nasir

Kungiyar da ke sa ido kan amfani da makaman guba a duniya, ta kuduri aniyar gudanar da bincike mai zurfi dan gano wadanda ake zargi da yin amfani da sinadaran guba na Chlorine gas a birnin Aleppo na kasar Siriya. A ranar talatar da gabata ne dai, masu aiyukan ceto a yankin Sukari kusa da inda ake gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen, suka ruwaito cewa jirage masu saukar ungulu sun yi ta sako gangunan sinadaran guba da ya yi mumunan illa ga lafiyar mutane sama da 80 yayinda mutum guda ya rasa ransa sakamakon shekar iskar guba.

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya za ta tabka mahawara dan tantance sahihancin rahotannin da hukumar kiyaye amfani da makaman guba suka gabatar, da ke zargin dakarun gwamnatin Bashar al-Assad da hannu dumu dumu wajen kai a hari da guba a yankin da 'yan tawaye ke rike da iko da su.

To sai dai dakarun gwamnatin na Siriya, sun musanta wannan zargin da ke cewa jiragen su ne suka kai harin sinadaran guba, inda suka ce 'yan tawayen na kora kunya ne dan ganin yadda ake samun nasara a kansu. Shekaru biyu da suka gabata ma dai an zargi gwamnatin Siriya da kai hare hare biyu na guba a yankuna bakwai a kasar da ke cikin rikici shekaru biyar.