Zaɓen Shugaban ƙasa da ′yan Majalisar Ghana | Siyasa | DW | 07.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaɓen Shugaban ƙasa da 'yan Majalisar Ghana

Akwai dai ƙalubale da dama na shugabanci da sabon shugaban zai fuskanta waɗanda su ka haɗa da batun tattalin arziƙi da na Ilimi da batun kiwon lafiya a faɗin Ghana.

A wannan Juma'ar ce al'ummomin Ghana su ka kaɗa ƙuri'unsu domin zaɓen shugaban ƙasa da kuma 'yan majalisun dokokin ƙasar.

'Yan takara da dama ne dai su ka shiga takarar musamman ma dai ta kujerar shugabancin ƙasar sai dai takara ta fi zafi tsakanin John Dramani Mahaman na jam'iyyar NDC wanda ke zaman shugaban ƙasar mai ci da kuma Nana Akufo Ado na jam'iyyar adawa ta NPP.

An samu ɗan jinkiri dai a farko gudanar da zaɓen a birnin Accra, fadar gwamnatin ƙasar saboda rashin akwatuna da katunan zaɓe a wasu mazaɓun da ke birnin.

Masu sanya idanu kan yadda zaɓen ya gudana a faɗin ƙasar sun shaida da cewar daga baya an shawo kan matsalolin da aka fuskanta, lamarin da ya sanya kaɗa aka cigaba da ƙuri'a kamar yadda aka tsara.

Rahotanni sun yi nuni da cewar ba'a gudanar da zaɓe a wasu cibiyoyi ba sakamakon matsalar da aka fuskanta na na'urorin da su ka ƙi amincewa da dangwala hannayen masu rijista.

Ana fatan cewar wannan zaɓen zai kasance wata dama ce da za ta daɗa ƙarfafa demokraɗiyyar wannan ƙasa da ake yabawa a yankin yammacin Afrika.

Akwai dai ƙalubale da dama na shugabanci da sabon shugaban zai fuskanta waɗanda su ka haɗa da batun tattalin arziƙi da na Ilimi da batun kiwon lafiya.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin