1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen shugaban ƙasa a Sabiya

January 19, 2008

Takara ta fi tsanani tsakanin Tadic da Nikolic

https://p.dw.com/p/Cupd
Boris Tadic shugaban SabiyaHoto: AP

►A yau ake gudanar da zaɓen shugaban kasa a Sabiya, inda ake takara tsakanin shugaba mai ci Boris Tadic da ɗan kishin ƙasa Tomislav Nikolic. Dukkan mutanen biyu dai suna adawa da bayawa lardin Kosovo ´yancin kai. To sai dai banbanci ra´ayi guda ɗaya mai muhimmanci tsakanin ´yan takarar biyu shi ne Tadic ya ƙudurin aniyar ƙarfafa hulɗa da ƙasashen yamma da kuma ƙungiyar tarayyar Turai. Tun yanzu kuwa ´yan siyasa a Sabiya da ƙasashen yamma suna kashedi cewa idan Nikolic yayi nasara to Sabiya ka iya zama wata saniyar ware kamar a lokacin Milosevic. ◄

Ko da yake ra´ayoyinsu kan batutuwa da dama sun bambamta amma akan batu ɗaya dukkan ´yan takarar neman kujerar shugaban ƙasar Sabiya sun haƙikance cewa Kosovo wani yanki ne na Sabiya. Cedomir Jovanovic ne kaɗai ke da ra´ayi na daban. Jovanonic wanda kasance abokin ɗasawar Firaminista Zoran Djindjic da aka yiwa kisan gillan yayi kira ga Sabiya da ta janye dukkan ikon da take da shi akan Kosovo mai rinjayen al´umar Albaniyawa.

Jovanovic:

Ya ce "A ra´ayina Kosovo ba Sabiya ba ce. Idan muna son Sabiya ta samu na cewa a Kosovo to ya zama wajibi mu haɗa kai da al´ummomin wannan lardi."

A bara jam´iyar Liberal Democrats ta Jovanovic a karon farko ta tsaya takarar zaɓen ´yan majalisar dokoki inda ta samu kashi biyar cikin 100 na ƙuri´un da aka kaɗa. To sai dai ba za ta kai labari ba a zaɓen shugaban ƙasar na yau lahadi. Ana sa ran yin gwagwarmaya ne tsakanin shugaba mai ci Boris Tadic da ɗan takarar masu matsanancin kishin ƙasa Tomislav Nikolic.

Tadic dai na matsayin mai goyon bayan ƙasashen yamma, inda ƙungiyar tarayyar Turai ke sa ran cewa zai taka rawa wajen ganin Sabiya ta bawa Kosovo ´yancin kai duk da adawa da ya nuna da haka a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Tadic:

Ya ce "Muna son Kosovo ta ci-gaba da zama cikin tarayyar Sabiya. A lokaci ɗaya kuma dole ne Sabiya ta ƙara samun kusanta da nahiyar Turai. Kwanciyar hankalin siyasa da ƙarfin tattalin arziki zai bawa Sabiya wata kyakkyawar makoma ta ruwa ga kowa da kowa."

A farkon wa´adin mulkinsa Tadic ya nuna alamun sassauci inda ya nemi gafara daga Kuratiya da Bosniya dangane da laifukan yaƙi da Sabiya ta aikata sannan kuma ya ba da cikakken haɗin kai ga Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya dake birnin The Hague inda ake ci-gaba da tsare shugaban jam´iyar masu kishin ƙasa Vojislav Sesely. Har yanzu kuwa shi ne shugaban jam´iyar wadda ta fi ƙarfi a Sabiya. Duk da cewa a ɓangaren ´yan adawa ta ke a majalisar dokoki amma tana sa ran yin wani abin ku zo ku gani a zaɓen shugaban ƙasar.

Sau biyu ɗan takararta Tomislav Nikolic ya tsaya mata takara, amma bai yi nasara ba. A wannan karo yayi alƙawarin sa ƙafar wando guda da masu cin hanci da rashawa da masu yiwa tattalin arziki zagon ƙasa.

Nikolic:

Ya ce "A matsayina na mai shekaru 55 na tsaya wannan takara ne domin in yaƙi rashin adalci da talauci da bauta da cin zalin da ake yiwa wasu daga cikin al´ummominmu. Saboda haka ina kira gareku dukka ku fita kaɗa kuri´a, domin akwai buki na gaba. Allah Ya ja zamanin Sabiya."

Masharhanta sun yi hasashen cewa zaɓen na yau ba zai fid da shugaba ba sai an yi zagaye na biyu nan da makonni biyu masu zuwa.