Zaɓen shugaban ƙasa a Belarussia | Labarai | DW | 19.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen shugaban ƙasa a Belarussia

A ƙasar Bellarussia, yau ne lahadi a ke gudanar za zaɓen shugaban ƙasa.

A jimilice, mutane fiye da million 7, ya cencenta su kaɗa kuri´u, a cikin runfunan zaɓe kussan dubu 7, domin fida gwani tsakanin yan takara 4, da su ka haɗa da shugaban mai ci yanzu, Alexandre Loukachenko, da ke bisa karagar mulki tun shekaru 12.

Shugaba Loukachenko, a wani taron manema labarai da ya kira jiya, ya yi alkawarin karya wuyan, yan adawa, muddun su ka ki amimcewa da sakamakon zaɓen.

Kamin a jefa kuri´un ma, mutane da dama na kauttata zaton, shugaban za shi tazarce ta ko wace hanya.

Madugun yan adawa Alexandre Milinkevich yayi kira ga magoya bayan sa, zuwa wata gagaramar zanga zanga muddun , hukumar zaɓe ta bayyana Alexandre Loukachenko, a matsayin wanda ya lashe wannan zaɓe.

Yan adawa na zargin shugaban, da tabka maguɗi, da kuma gudanar da kwaskwarima, ga kundin tsarin mulki na ƙasa, wanda a yanzu ya bashi damar shiga zaɓe har tsawan rayuwar sa.

A karfe 6 agogon GMT za a rufe runfunan zaɓen.