Zaɓen Gini ya ɗauki hankalin masharhanta | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 19.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Zaɓen Gini ya ɗauki hankalin masharhanta

Mutumin da ya daɗe yana jagorantar 'yan adawa, Alpha Conde shi ya lashe zaɓen shugaban ƙasa

default

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Gini Alpha Conde a tsakiyar magoya bayansa a birnin Konakry

A wannan makon dai jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne a ƙasar Gini inda a cikin makon aka sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar. A rahotonta jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara ne da ambatar Alpha Conde a matsayin zaɓaɓɓen shugaban Jamhuriyar Gini. Ta ce bayan ya shafe shekaru da yawa a matsayin jagoran 'yan adawa yanzu haƙan Conde mai shekaru 72 ya cimma ruwa. Jaridar ta ce wannan dattijon yana iya buga ƙarji da kasancewa mutumin da ya lashe zaɓen da aka ce an kamanta adalci a cikinsa a tarihin wannan ƙasa dake yankin yammacin Afirka da ta samu 'yancinta daga Faransa kimanin shekaru 52 da suka gabata.

To sai dai a nata rahoton jaridar Neues Deutschland cewa ta yi lashe zaɓen da Conde yayi ya janyo tashin-tashina a Gini. Ta ce lalle ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare, domin sakamakon farko ya sanya tsohon Firaminista Cellou Dalein Diallo a gaba, amma da tafiya ta yi tafiya Alpha Conde ya cimma masa har ma ya tsere ma sa. Jim kaɗan bayan sanar da sakamakon zaɓen, Conde ya yi magana da cewa an buɗe wani sabon babi a tarihin ƙasar sannan yayi kira ga abokan hamaiya da su ba shi haɗin kai yana mai cewa lokaci yayi na miƙa hannun zaman lafiya.

Madagaskar Wahlen 2010 Referendum

Masu kaɗa ƙuri'a lokacin zaɓen raba gardama kan kundin tsarin mulkin Madagaskar a birnin Antananarivo

Yunƙurin juyin mulkin soji a Madagaskar, inji jaridar Tageszeitung tana mai nuni da boren da wasu sojoji ƙarƙashin jagorancin Janar Noel Rakotonandrasana suka tayar a ranar da ƙasar ta shirya gudanar da wata ƙuri'ar raba gardama kan kundin tsarin mulkin ƙasa. Sojojin da suka yi wannan yunƙurin su ne suka ɗora gwamnatin mai ci kan kujerar mulki a wannan tsibiri na Madagaskar. Tun a watan Maris ɗin shekarar bara ƙasar ta tsunduma cikin rikici bayan juyin mulkin da sojoji suka yiwa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Marc Ravalomanana sannan suka ɗora magajin garin babban birnin ƙasar Andre Rajoelina kan kujerar shugaban ƙasa. A cikin watan Satumba shugaban ya bari wani taron ƙasa ya amince da shirya ƙuri'ar raba gardama kan sabon daftarin kundin tsarin mulki akan shirye-shiryen zaɓen da ƙasar za ta gudanar a baɗi. Daftarin ya rage shekarun tsayawa takara daga 40 zuwa 35 domin bawa shugaba Rajoelina mai shekaru 36 damar yin takara. Jarida ta ce babu wanda zai iya hasashen abin da zai faru a ƙasar nan gaba kaɗan.

Namibia / Flughafen / Windhuk / Terror

Filin sukar jiragen saman birnin Windhoek na ƙasar Namibiya

A karon farko Namibiya ta ɗauki hankalin masu yaƙi da ayyukan tarzoma na ƙasa da ƙasa inda ake zargin ƙungiyar al-Shabab ta Somaliya da hannu bayan gano wani akwati ɗauke da bam da aka yi niyar sanyawa cikin wani jirgin sama da ya nufi nan Jamus. A rahotonta jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi ko da yake an jima ana kyautata zato masu tsattsauran ra'ayi ka iya amfani da wannan ƙasa wajen aikata ta'asarsu amma kawo yanzu ba wata ƙwaƙƙwarar shaida da ta tabbatar da wannan zargi. Amma yanzu haka jami'in leƙan asirin Jamus suna cikin ƙasar don gudanar da bincike kan wannan akwati.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi