Zaɓen gama gari a Burkina Faso | Labarai | DW | 29.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen gama gari a Burkina Faso

Al'umma a Burkina Faso na ci gaba da kaɗa ƙuria a zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokoki.

Burkina Faso Wahl in Ouagadougou Präsdentschaftskandidat Zephirin Diabre

Dan takara shugaban ƙasa Zephirin Diabre na kaɗa ƙuria

Kimanin mutane miliyan biyar ake sa ran za su fito a zaɓen wanda a da aka so yin shi a cikin watan jiya amma daga bisani aka ɗage saboda juyin mulkin da sojoji suka yi

Yan takara guda 14 za su fafata a zaɓen,kuma ana sa ran biyu daga cikinsu Roch Marc Christain Kabore tsohon firaminista a gwamnatin Blaise Compaoré da wani ɗan kasuwar Zéphirin Diabré za su iya samu nasara. A cikin watan Oktoba na shekara bara ne wani boren al'umma ya share gwamnatin Blaise Compaore a kan yunƙurinsa na yin wani sabon wa'adi bayan yayi shekaru 27 a kan karagar mulki