Zaɓe a kewayen birnin Tokyo
April 23, 2006Talla
Jam´iyar Praminista Junichiro Koizumi na kasar Japon, ta sha kayi, a zaɓen yan majalisun dokoki, da ka gudanar yau, a wasu yankuna na kewayen birninTokyo.
Hukumar zaɓe ta bayyana Kazumi Ota, ta jam´iyar adawa a matsayin wadda ta samu kujerar wakilici wanna yanki amajalisar dokoki kasar.
Kafofin sadarwa a ƙasar Japon, na kwatatanta wannan kayi, da jam´iyar PLD ta sha, a matsayin wata alama, mai nuna dushewar kwarjinin Praminista Koizumi , da ke shirin barin mulki, a watan satumber mai zuwa.