SiyasaJamus
Yunwa ta karu a kasar Mali
December 9, 2021Talla
Bayanai na nuna cewa ana ci gaba da samun karuwar wadanda ke fama da yunwa a kasar Mali.
Sabbin alkaluma sun una cewa adadin su ya karu da mutum miliyan daya da dubu 200 a bana.
Ana dai alakanta karuwar fama da karancin abincin ne a Mali da matsalolin tsaro da rashin kyawun damina da ma ta annobar corona.
Kungiyoyin agaji 22 da ke aikin jin kai a kasar ne dai suka ce hakan a wani rahoto da suka fitar.
Tuni ma dai mutum dubu 400 suka tsere daga kasar, inda farashin abinci ke ci gaba karuwa a kullum rana ta Allah.
Fari kuma ya lalata sama da hekta dubu 225 ta filayen noma.
Kungiyoyin na agaji, na cewa hare-haren 'yan bindiga na hana su iya kai dauki a yankunan da matsalar ta fi kamari a Malin.