1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa bai kare ba a Aljeriya

Mahmud Yaya Azare
March 21, 2019

A Aljeriya mukarraban shugaban kasa Abdelaziz Bouteflika na ci gaba da yin wasiyar aniyarsa ta yi tazarce duk da fuskantar mummunar zanga zangar da yake yi, kan tsawaita wa,adin mulkinsa da yayi

https://p.dw.com/p/3FQvI
Algerien Algier - First Friday Rally
Hoto: Getty Images/AFP/R. Kramdi

Sai dai dukkanin alamu sun nunar da cewa shugaban da ya yi wa'adin mulki hudu ya kama hanyar  jefar da mangwaro don ya huta da kuda.

Jaridar Annahar da ta saba labarto abubuwan da ke faruwa a fadar mulkin kasarce dai ta wallafa a shafinta na safiyar yau Alhamis cewa, Shugaba Boutifilikan na shirin sanar da aniyar  sauka daga kan mulki karshen wa,adin mulkinsa dake karewa ran 28 ga watan Afrilu .

Wakiliyar tashar TV Farance 24 da ke daukar labarai daga fadar mulkin ta Aljeriya  tayi karin bayani kan wannan batun kamar haka:

Ta ce "Shugaban zai dauki wannan matakin ne sakamakon rashin amincewa da masu zanga-zanga suka yi da shirinsa na tsawaita wa,adinsa har zuwa shekara daya, don gudanar da taron kasa da yin garambawul ga kundin tsarin mulki kana a gudanar da zaben shugaban kasar dashi bazai tsaya takara cikinsa ba, kudurorin da masu zanga zangar sukai fatali dasu.”

Algerien | Abdelaziz Bouteflika
Shugaba Abdelaziz Bouteflika na AljeriyaHoto: imago/photothek/T. Trutschel

Fitowar wannan sanarwar na zuwa ne jim kadan bayan da jam,iyya mai mulki a kasar, National Liberation Front, ta yaye wa Bouteflikan baya, yadda kakakinta Mu,az Bu Sharib ya ce suna tare dari bisa dari da masu zanga zangar:

"Yayan jam,iyarmu suna goyan bayan wannan fafutukar da masu zanga-zangar ke yi, sake ba kaidi. Muna kuma goyan bayansu da zuciya daya, gami da fatan ganin an cimma muradun da suke fafutuka kansa  ta hanayar shata taswirar hanyar da zata fayyace yadda za,a gudanar da  komai dalla dalla.”

 Ita ma jam,iyya ta biyu a kawancen jam,iyyu masu mulkin kasar, National  Rally for Democracy, ta sanar da ficewarta daga kwalalan na Boutefilikan da ke tangal-tangal din kifewa, kamar yadda kakakinta, Siddeq Shihab ke fadi:

Algerien Algeir - Proteste gegen Abdelaziz Bouteflika
Gangamin adawa da mulkin Bouteflika Hoto: Reuters/Z. Bensemra

"Tsayar da Boutefilika  takara karo na biyar da mukai, a cikin wannan yanayin da yake ci, bacewar basira ne da ganganci.

Shi ma Babban Hafsan sojin kasar, Ahmad Qayeed Saleh, a wata sabuwar sanarwar da ya fitar jiya,da ke nuna goyan bayansa ga masu zanga-zangar a karon farko, ya ce  suna da kyakkyawar manufa.