Yunkurin tallafawa wanda ke cikin matsi | Labarai | DW | 08.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin tallafawa wanda ke cikin matsi

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta mika kokan bararta don samun dalar Amirka miliyan dubu 16 da rabi da za ta yi amfani da su domin tallafawa al'ummar da yaki ya tagayyara.

Shugabar hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos ta ce za su batar da kusa rabin kudin da suke bukata ne kan wadandan yakin da ake yi a Siriya ya tagayyara duba da irin dimbin bukatun da suke da su.

Amos ta ce inda kudin sun samu, kusan mutane miliyan 60 ne a shekara mai kamawa za su amfana daga irin tallafin da za su bada daga cikin mutum miliyan 78 da ke warwaste a cikin kasashe 22.

To sai dai wannan tallafi da ake son badawa in kudin sun samu ba su hada da wanda ke cikin matsi a Djibouti ba da ma wanda rikici ya raba da muhallansu a yankin Sahel musamman tarayyar Najeriya da Mali, amma hukumar ta ce za ta nemi tallafi na musamman cikin watan Fabrairun badi don agaza musu.