Yunkurin Palesdinawa na samun kasa | Labarai | DW | 04.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin Palesdinawa na samun kasa

Palesdinawa sun tsayar da ranar da za su fara aiwatar da tsarin da zai basu damar samar wa kansu da kasa mai cin gashin kanta.

Kungiyar Hadin Kan Palesdinawa ta tsayar da wannan wata na Nuwamba a matsayin lokacin da za ta shigar da kudiri gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin samun damar kawo karshen mamayar da Isra'ila ke yi mata. Wani kusa na kungiyar mai suna Wassel Abou Youssef ya yi wannan bayani a Ramallah, bayan da aka tashi dutse hannu riga a tattaunawar da aka yi tsakanin sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry da wakilin OLP Saeb Erakat.

Ita dai kasar Amirka ta na nema Kungiyar Hadin Kan Palesdinawa ta koma kan teburin sulhu da Isra'ila, duk kuma da rashin samun nasara a tattauanwar da suka gabata a baya tsakanin bangarorin biyu da ke gaba da juna.

Palesdinu ta tanadi bin matakai uku wajen samun 'yancin cin gashin kai, daga ciki kuwa har da samun hadin kan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Ko kuma shiga cikin kungiyoyi ko hukumomi na kasa da kasa ciki har da kotun hukuntan manyan laifukan yaki.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu