Yunkurin kai wa al'ummar Siriya tallafi
July 12, 2014Kwamitin sulhu na Majalisaar Dinkin Duniya na shirin dubawa tare da amincewa da wani kuduri da zai bai wa jami'an bada agaji damar shiga Siriya daga Turkiyya da Iraki da kuma Jordan don tallafa wa al'ummar kasar da ke cikin matsananciyar bukata.
Wannan yunkuri dai ya biyo bayan tattaunawa da Australiya da Jordan da Luxembourg suka yi ta tsawon makwanni inda daga bisani suka fidda wani daftari kan wannan batu wanda za a kada kuri'ar amincewa da shi ranar Litinin idan Allah ya kaimu.
Rasha wadda ke dasawa da gwamnatin Bashar al-Assad ta ce ba ta da wani shiri na hawa kujerar naki kan wannan batu, ko da da shi ke jakadanta a zauren na Majalisar ta Dinkin Duniyar Vitaly Churkin ya ce akwai wasu batutuwa biyu da ke cikin daftarin wanda ba su kai ga amincewa da su ba.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce idan wannan yunkuri ya tabbata kimanin mutane miliyan daya da rabi ne galibi fararen hula wanda ke zaune a yankunan da ke hannun 'yan tawaye za su amfana da shirin wanda zai samar musu da abinci da maganguna.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe