1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTunusiya

Tunusiya: Cafke lauyoyi da 'yan jarida

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 17, 2024

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da kame wasu lauyoyi da aka yi a Tunusiya, tana mai bayyana tsare sun da keta tsarin doka a kasar da ke yankin arewacin Afirka.

https://p.dw.com/p/4g0Ia
Ravina Shamdasani | Majalisar Dinkin Duniya | Tunusiya
Mai magana da yawun ofishin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Ravina ShamdasaniHoto: Fatih Erel/AA/picture alliance

Mai magana da yawun  ofishin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniyar Ravina Shamdasani ce ta bayyana hakan ga manema labarai a birnin Geniva na kasar Switzerland, inda ta ce matakin na nuni da fin karfi da cin-zarafin dan Adam. Rahotanni sun nunar da cewa a makon da ya gabata ne aka kai samame kan kungiyar lauyoyi ta Tunusiyan, wanda Majalisar Dinkin Duniyar ta bayyana da ya saba ka'idojin dokokin kasa da kasa kan bayar da kariya da kuma 'yancin lauyoyi. Wadanda mahukuntan na Tunusiya suka cafke tare da tsareawa dai, sun hadar da 'yan jarida da kuma masu sharhi kan al'amuran siyasa.