Yunkurin dakile kungiyar ′yan tawayen Seleka | Siyasa | DW | 31.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yunkurin dakile kungiyar 'yan tawayen Seleka

A kokarin da kasashen duniya ke yi na warware rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, dakarun Kamaru sun rusa sansanin 'yan tawayen da ke cikin yankunan kasar.

Dakarun kasar Kamaru sun bayyana samun nasarar lalata wani sansanin 'yan tawayen kungiyar Seleka da ke yakunan kasar. Sojojin, sun kuma sanar da kwace makamai masu yawa da kuma cafke mambobin kungiyar da dama, game da kissan daya daga cikinsu. Sai dai kuma shaidun gani da ido suka ce gawarwarki takwas ne suka gani na 'yan tawayen da cibiyarsu ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Mazauna kauyen Kette da ke yankin gabashin Jamhuriyar Kamaru kenan ke nuna farin cikinsu ga dakarun kasar cikin manyan motoci, wadanda suka tarwatsa wani sansanin 'yan tawayen Seleka, da ke gujewa shirin kwance damarar da dakarun Faransa da na tarayyar Afirka ke yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Daya daga cikin mazauna kauyen, mai suna Lizette Atou, ta ce ko da shike karar harbe harben bindigogi ne ta tayar dashi daga barci a ranar Lahadi (29. 12. 13), amma yana farin cikin ganin cewar, a yanzu matsalar ta kawo karshe:

Ta ce "Dakarun Kamaru sun yi namijin kokari wajen kare kansu. Sun kuma yi narasar kwace makamai da kuma kissan daya daga cikin 'yan tawayen. Tilas ne gwamnatin Kamaru ta yi hubbasa wajen dakile 'yan kungiyar Seleka domin daidaita lamura a kasarmu."

Fito na fito a tsakanin Kamaru da Seleka

Wannan dai ba shi ne karo na farkon da ake yin gumurzu a tsakanin dakarun Kamaru da kuma 'yan tawayen da suka fito daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kuma a yankunan Kamaru ba. Wani harin da sojoji suka kaddamar a cikin watan Nuwamba, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida, biyar daga cikinsu kuma ana zargin mambobin kungiyar Seleka ne, yayin da guda kuma sojan Kamaru ne.

Kazalika, sojojin na Kamaru sun sake kwato wani wurin hako zinare da ke Kana, wani garin da ke kusa da iyaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Bayan hare haren baya bayannan ne kuma gwamnan yankin gabashin Kamaru Ivaha Dieudonne ya sanar da nasarar kwace makamai da dama daga hannun 'yan tawayen na Seleka, wadanda ya ce sun dade suna muzguna musu.

Ya ce " Ba ma son mugayen baki anan. Sun zaci cewar za su zo wannan yankin ne su yi abin da suka ga dama, amma mun dauki dukkan matakan da suka wajaba domin tabbatar da tsaron al'ummar yankin gabashi. Jami'an tsaronmu ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yin sintiri a wurin."

Zentralafrikanische Republik Michel Djotodia

Shugaba Michel Djotodia na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Alwashin kawar da kungiyar Seleka

A makon jiya ne gwamnatinn Kamaru ta sanar da bude sansanin mayakan sama a yankuna da ke fama da rigingimu,tare da tura dakarun rundunar ko ta kwana domin hana 'ya tawayen kungiyar Seleka ta Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya ci gaba da kutsawa cikin wasu yankunan Kamaru, game da mayar da yankunan a matsayin tudun mun tsira a garesu, da kuma sansanin bayar da horo. Da safiyar wanan Litinin (30. 12. 13) ce kuma ministan tsaron Kamaru Edgard Alain Mebe Ngo ya ziyarci yankin gabashin Kamaru, inda ya baiwa mazauna yankin tabbacin tsaron lafiya da dukiyarsu:

Ya ce Ina tabbatar muku da cewar, bisa la'akari da irin tanadin da muka yi wa Bertoua, hedikwatar yankin gabashin Kamaru ta fuskar tsaro da kuma dakarun da muka jibge anan, a yanzu yankin ne ya fi tsaro a daukacin yankunan Kamaru. Saboda haka ku kawar da duk wata fargabar kariya da ta tsaro."

Kokarin kwance damarar mayaka a Jamhuriyar Afirka Ta tsakiya dai, ya jefa matsalar tsaro ga kasashen da ke makwabtaka da ita.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin