Yunkurin ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran | Labarai | DW | 06.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran

Amirka a karon farko karkashin jagorancin gwamnatin Joe Biden za ta halarci wani taron tattaunawa kan yiwuwar ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Masu aiko da rahotanni sun ce Iran da Amirkar ba za su hadu kai tsaye a yayin tattaunawar ba, to amma tawagogin kasashen Turai ne za su kasance masu shiga tsakani a yunkurinsu na sake dawo da yarjejeniyar, wacce tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya yi fatali da ita a baya.

Daukacin manyan kasashen duniya da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar ta Viennan dai irin su Jamus Faransa da Birtaniya da Rasha da China za su halarci wani taron, a yayin da a share daya wasu kwarru daga Amirkar za su gabatar da nasu taron amma ba tare da Iran ba.