1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yuganda za ta dawo da alaka da Ruwanda

January 23, 2022

Dan shugaban kasar Yuganda Muhoozi Kainerugaba ya isa Ruwanda don ganawa da shugaba Paul Kagame, ziyarar da ke nuna alamun dawowar dangantaka tsakanin kasashen.

https://p.dw.com/p/45xjZ
Yuganda |Janar Muhoozi Kainerugaba
Hoto: Lubega Emmanuel/DW

Ana dai sa ran Kainerugaba wanda janar din soja ne kuma ake jita-jitar yiwuwar ya gaji mahaifinsa Yoweri Museveni a shugabancin Yuganda, ya gana da shugaba Kagame.

An dai kwashe tsawon kimanin shekaru uku kenan da rufe kan iyakokin kasashen biyu tare da datse dukkan wata hulda ta kasuwanci.

Kasar Yuganda ta zargi makwabciyarta Ruwanda da yi mata leken asiri tare da kashe wasu 'yan kasar biyu a wancan lokacin, zargin da Ruwandar ta musanta. Dangantaka ta kara yin tsami tsakanin kasashen a bara lokacin da bincike ya gano Ruwanda na amfani da manhajojin kasar Isra'ila wajen leken asiri tare da yin kutse cikin wayoyin firanministan Yuganda da wasu kusoshin gwamnati.