Yuganda na son toshe shafukan sada zumunta | Labarai | DW | 12.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yuganda na son toshe shafukan sada zumunta

Hukumar kula da sadarwa a kasar Yuganda ta bukaci kamfonin sadarwar zamani su toshe kafiofin saboda fargabar tashin hankalin zabe gabanin zaben shugaban kasa.

Ma'aikatar kula da sadarwa a Yuganda ta aike wa kamfanin Facebook wasika ta musamman, inda take neman rufe shafuka gabannin ranar zabe saboda fargabar amfani da su wajen tada hankali yayin zabe ko bayan zaben.

Tuni Facebook ya fara daukar matakan toshe wasu shafukan da ke yada labaran karya, da masu amfani da shafuka fiye da guda daya. A ranar 14 ga Janairu 2021 kasar Yuganda za ta gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki.

Sai dai hankali ya fi karkata ne kan karawa tsakanin Shugaba mai ci Yoweri Museveni da ke neman wa'adin mulki na uku, da kuma fitaccen mai adawa Boyi Wine.