Yuganda: Harin bam ya firgita al'umma | Labarai | DW | 16.11.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yuganda: Harin bam ya firgita al'umma

Wasu abubuwa masu fashewa guda biyu da suka tarwatse a Kampala babban birnin kasar Yuganda, sun razana mutane. Rahotanni sun nunar cewa, an ga gawarwakin mutane biyu bayan harin.

Hukumomin kiwon lafiya sun ce kimanin mutane 24 suke bai wa kulawar gaggawa, bayan harin da kawo yanzu ba bu tabbaci kan wadanda suka kaddamar da shi. Sai dai mataimakin shugaban 'yan sandan kasar Edward Ochom ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, suna gudanar da bincike kan lamarin. 

Daya daga cikin ababen fashewar dai ya tarwatse ne a kusa da ginin majalisar dokokin kasar, yayin da dayan kuma ya tarwatse a kusa da wani caji ofis na 'yan sanda. Yuganda dai na ci gaba da fuskantar hare-hare na bama-bamai a cikin makonnin baya-bayan, inda sojojin kasar suka kwashe tsawon lokaci suna artabu da mayakan kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qaida da ta addabi kasar Somaliya.