Yuganda: Bobi Wine ya zargi gwamnati | Labarai | DW | 11.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yuganda: Bobi Wine ya zargi gwamnati

Babban dan takarar adawa a zaben shugaban kasar Yuganda na ranar Alhamis mai zuwa Robert Kyagulanyi da ake wa lakabi da  Bobi Wine ya yi ikirarin shi mutum ne mai bin doka da oda.

A wata hira ta musamman da Bobi Wine din ya yi da DW a wannan Litinin Bobi Wine wanda mawaki ne ya ce duk da cewa dokokin Yuganda sun amince ma sa ya yi yakin neman zabe amma gwamnati na kawo masa cikas.

''Shugaba Museveni ya lalata gaba daya hukumomin kasar, kuma yana mulki irin na kama-karya ta hanyar mayar da majalisa 'yar amshin shata, hatta bangaren shari'a, Museveni ya ya sanya su a aljihunsa.'' inji Bobi Wine

Bobi Wine dai ya ce  irin wannan dabi'u da Shugaba Museveni ke nuna wa su ne za su kayar da shi a zaben da ke tafe.