1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yousafzai ta ziyarci mahaifarta a Pakistan

Yusuf Bala Nayaya
March 31, 2018

Malala Yousafzai ta fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa ta bar Swat ido rufe yanzu kuma ta dawo ido bude.

https://p.dw.com/p/2vI9G
Pakistan Malala Yousafzai in Heimatstadt Mingora im Swat Valley
Hoto: DW/Adnan Bacha

Malala Yousafzai ta ziyarci lardin kwarin Swat a wannan rana ta Asabar, ziyarar da ke zama ta farko tun bayan dauketa daga yankin sakamakon harbin bindiga da ta sha a hannun mayakan Taliban sama da shekaru biyar da suka gabata.

Malala ta fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa ta bar Swat ido rufe yanzu kuma ta dawo ido bude, ma'ana ta fita ba tare da sanin halin da take ciki ba. Matashiyar da ke zama 'yar fafutikar ganin yara mata sun je makaranta ta samu rakiya ta iyaye da yayunta da jami'an tsaro inda ta gana da iyalai da abokan arzuka cikin farinciki da annashuwa kafin daga bisani ta koma birnin Islamabad na Pakistan.