Yiwuwar samun hadin kai a Iraqi | Labarai | DW | 15.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yiwuwar samun hadin kai a Iraqi

Alamu na nuni da cewar akwai yiwuwar a samu gwamnatin hadin kai tsakanin Musulmi mabiya Shi'a da Sunna a Iraqi.

Manyan shugabannin kabilu da malaman addini na Musulmi mabiya Sunna a Iraqi sun amince su shiga a dama da su a sabuwar gwamnatin kasar karkashin Firaminista Haider al-Abadi da ke zaman Musulmi mabiyin Shi'a. A baya dai shugabannin al'ummar Musulmin Iraqin mabiya Sunna sun kasance masu matukar adawa da gwamnatin Firaminista Nuri al-Maliki da shima ke zaman Musulmi mabiyin Shi'a. Sai dai kuma sun gindaya sharidin da zai sanya su kasance cikin gwamnatin karkashin Musulmi mabiya Shi'a inda suka bukaci al-Abadi da ya tabbatar da kare 'yancin al'ummar da ba ta da rinjaye a kasar. A wata hira da ya yi a gidan talabijindaya daga cikin manyan malamai kuma jagoran Musulmi mabiya Sunna 'yan kabilar Dulaimi a gundumar Anbar Ali Hatem Suleiman ya ce batun ko za su shiga a dama da su wajen yakar 'yan kungiyar ta'addan IS wani batu ne da zai zo nan gaba. Gundumar ta Anbar dai ta kasance yankin da Musulmi mabiya Sunna ke da rinjaye a Iraqin.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu