Yawan kuɗi da ake kashewa a fannin tsaro | Siyasa | DW | 02.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yawan kuɗi da ake kashewa a fannin tsaro

cibiyar nazarin harkokin zaman lafiya ta ƙasa da ƙasa ta gano yawan kuɗi da ƙasashen duniya suka kashe a bara.

default

Cibiyar, wadda aka fi sani da Stockholm International Peace Research Institute dake da mazauni a birnin Stockholm na ƙasar Sweden, ta fitar da rahon dake cewar, yawan kuɗaɗen da ƙasashen duniya suka sanya a fannin soji ya kai dala Zambar ko kuma trilion ɗaya da miliyan dubu 530 a bara kaɗai.

Rahoton ya ce sakamakon nazarin ya gano cewar, an sami ƙaruwar kusan kashi shidda cikin 100 a shekara ta 2009 idan aka kwatanta da shekara ta 2008. Sam Perlo - Freeman shi ne kakakin cibiyar, wadda a taƙaice ake ƙira SIPRI ya yi ƙarin haske akan rahoton:

" Koma bayan tattalin arziƙin da duniya ta faɗa ciki, bata yi wani ta'asirin a zo a gani ba ga yawan kuɗin da ƙasashe ke kashewa a ɓangaren soji. Ko da shike za'a ga wannan batun a matsayin abinda ya saɓawa tunani bisa la'akari da rikicin tattalin arziƙin, amma kuma ya dace da irin matakan da gwamnatoci ke ɗauka domin daidaita harkokin tattalin su, kasancewar basu rage yawan kuɗin da suke kashewa a ɓangaren kyautata rayuwar jama'a ba.

Schweden Logo Friedensforschungsinstitut SIPRI

Cibiyar da ta wallafa rahoto

Ƙasar Amirka ce ke kan gaba wajen kashe ɗimbin kuɗi a harkar soji, inda rahoton ya ce kashi 54 cikin 100 na yawan abinda aka kashewa harkar sojin ya fito ne daga ita Amirkar, abinda cibiyar ta ce dama ta saba da yin hakan, a yayin da ƙasar China kuwa ke rufa mata baya a matsayi na biyu, kana Faransa ta zo ta ukku, kakakin cibiyar ya ce, da alama Amirka ta ƙuduri anniyar ci gaba da riƙe kambin ne:

"A cikin lokaci mai tsawo, Amirka ta ƙuduri anniyar yin kane kane a fannoni daban daban na harkokin soji domin shirin ko ta kwana. Wannan ƙudurin kuma bai sauya ba, ko dai a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaba Clinton ne ko Bush koma Obama dake mulki a yanzu saboda haka ko da shike hukumomin Amirka na ƙokarin rage giɓin kasafin kuɗinsu a shekara mai zuwa, amma kuma suna ci gaba da kashe ɗimbin kuɗi ga fannin soji."

UN-Konferenz zu illegalen Kleinwaffen

ƙananan makaman yaƙi

Sauran ƙasashen dake cikin rukunin ƙasashe 10 dake sahun farkon kuwa, sun haɗa da Birtaniya, Japan, Jamus, Saudiyya da Indiya da kuma Italiya, inda kakakin cibiyar ta SIPRI Sam Perlo - Freeman ya ce, hukumomin Jamus sun mayar da hankali ne ga bayar da horo ga dakaru:

"Ga jamus kuwa bunƙasar da aka samu, ta kasance ne a fagen kashe kuɗaɗen wajen bayar da horo a fannin soji, wanda ya haura zuwa kimanin kashi ukku cikin ɗari a shekara ta 2009.

Babban dalilin daya sa ƙasashe ke kashe ɗimbin kuɗi wajen shigo da makamai dai a cewar rahoton, shi ne albakatun mai da iskar Gas da kuma sauran albarkatu. Sai dai kuma cibiyar binciken ta gano cewar, ko da shike ƙasashe irin su Nijeriya da Rasha sun ƙara yawan kuɗin da suka kashe a harkar makamai a bara, amma bai kai yadda suke kashewa a shekarun baya ba. Kazalika cibiyar ta gano cewar, Rasha da Amirka ne ke kan gaba wajen sayar da makamai zuwa ƙetare.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Ahmad Tijjani Lawal