Yaushe za a tsagaita wuta a Gaza?
September 10, 2024Talla
Da yake magana da manema labarai, ministan harkokin tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce akwai haske kan cimma tsagaita bude wuta na tsawon makonni shida, har ma yuwar sako 'yan Isra'ila da a ke tsare da su a zirin Gaza tare da samar da zaman lafiya a yankunan da ke kusa da arewacin kasar Lebanon.
Ministan ya kara da cewa, Isra'ila ba za ta yi alkawarin kawo karshen luguden wuta a Gaza na din-din-din ba, kamar yadda kungiyar Hamas ta gindaya a sharudan yarjejeniyar.
Jami'an agaji a Khan Younis sun ce dakarun isra'ila sun yi barin wuta a tuddan na tsira da ke zirin Gaza, wanda ya kashe mutane akalla 40 wasu 60 sun jikkata.