Yau ta ke babban zabe a kasar Isra′ila | Labarai | DW | 17.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yau ta ke babban zabe a kasar Isra'ila

An fara kada kuri'a a, inda tuni mutane suka fara zuwa rumfunanan don zaban sabuwar gwamnatin, shekaru biyu bayan rusa majalisar kasar

Zaben kasar ta Isra'ila dai anana ganin za a kankan-kan tsakanin firaminista mai ci Benjamin Netanyahu da kuma Isaac Herzog. Da safiyar yau Talatan ne aka fara shiga rumfunan zabe a kasar ta Isra'ila, don kada kuri'u cikin shekaru biyu bayan rusa majalisar kasar da faraiminista Benjamin Netanyahu ya yi sakamakon rushewar gwamnatinsa ta hadaka.

Mr. Netanyahu na jami'yyar Likud, na neman zabe karo na hudu kenan, inda wasu manazarta ke cewa yana da rinjaye a majalisar kasar, sai dai yana fuskantar barazanar adawa daga jam'iyyar nan ta Zionist wanda Isaac Herzog ke jagoranta.

A jiya Litinin ne dai, aka jiyo Faraimnistan Benjamin Netanyahu na Isra'ila na cewa, muddin ya lashe zaben to kuwa babu batun kasar Falasdinu.