Yarjejeniyar tsagaita wuta a Yaman ta fara aiki | Labarai | DW | 15.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Yaman ta fara aiki

Yarjejeniyar ta soma aiki ne a daidai lokacin da aka fara yin wani taro a Switzerland domin warware rikicin ƙasar.

Wakilai na gwamnatin Yaman da na 'yan tawaye sun fara tattaunawar samar da sulhu a Switzerland a ƙarkashin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya.Wannan taro na zuwa ne daf da lokacin da mai shiga tsakanin na MDD Ismail Ould Cheik Ahmed ya sanar da cewar yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki bakwai da aka cimma tsakanin ɓangarorin da ke gaba da juna ,ta fara aiki a yau da misalin karfe 12 na rana.

Tun a cikin watan Maris da ya gabata ake gwabza faɗa tsakanin dakarun gwamnatin 'yan Sunni masu samun goyon bayan Saudiyya,da kuma dakarun 'yan tawaye na Houthis 'yan Shi'a masu samu tallafin ƙasar Iran.kawo yanzu mutane sama da dubu biyar suka rasa rayukansu a cikin tashin hankalin galibi fararan hula