Yarjejeniyar tsagaita wuta a Bangui | Labarai | DW | 05.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Bangui

Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyoyin ‘yan tawayen kasar a Khartoum babban birnin  kasar Sudan

Tun bayan hambare gwamnatin tsohon shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Francois Bozize daga mulki a shekarar 2013, kasar ke fama bulluwar kungiyoyin sa kai masu dauke da makamai, wadanda ke rike da kashi 80 cikin dari na fadin kasar.

Yarjejeniyar wacce ke karkashin jagorancin kungiyar Tarayyar Afirka ta AU, ta kai ga shawo kan kungiyoyin ‘yan tawaye 14 da ke gwaggwarmaya ya zuwa ga samun masalahar ne, kwanaki bayan an yi hannun riga kan batun raba mukamai da batun yafiya ga shugabannin kungiyoyin masu yakin sunkuru.