Yarjejeniyar tsagaita wuta a arewacin Mali | Labarai | DW | 23.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar tsagaita wuta a arewacin Mali

'Yan tawayen da suka karbe iko da garin Kidal a arewacin Mali bayan sun fatattaki sojin gwamnati a wata arangama sun amince da shirin tsagaita wuta a wannan Juma'ar.

A zantawarsa da kamfanin dillacin labari na AFP, guda da cikin jami'an diflimasiyyar da suka hallarci zaman ya ce wannan cigaba da aka samu ya biyo bayan ziyarar shugaban kungiyar kasashen Afirka ta AU Mohammed Ould ABdel Aziz ya kai zuwa Kidal din a yau.

Yayin ziyarar ta dai, shugaban na AU da gami da shugaban kungiyar dakarun wanzar da zaman lafiya ta MINUSMA Bert Koenders sun tattaunawa da 'yan tawayen inda nan ne suka cimma wannan yarjejeniya.

Yarjejeniya da aka cimma dai ta nemi 'yan tawaye da su kasance inda suke yanzu haka maimakon cigaba da mamaye arewacin kasar kamar yadda suka lashi takobin yi a baya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu